top of page

Shin ko man kadanya yana maganin COVID-19? A’a ba haka ba ne

Mohammed Auwal Ibrahim

Wednesday, 6 May 2020

Yawan yaduwar labaran kanzon kurege da jita-jita akan cutar COVID-19 musamman ta bangaren “maganin” cutar ya dan ragu kadan, idan aka kwatanta da watan baya (Maris 2020). Wannan kokari ne na gwamnati, masana ilmin kimiyyah, maaikatan lafiya, kungiyoyi masu zaman kansu, da sauransu, bisa kiraye-kirayen wayar da kai da suke yi akan cutar. Amma kuma duk da haka akwai sauran yaduwar wasu zantuka marasa tushe kuma masu razanarwa dangane da maganin COVID-19. Daya daga cikin wadannan zantukan shine (wai) man kadanya yana “kashe” kwayar halittar coronavirus, kuma yana bada “kariya” ga cutar idan har an shafa a hannu, hanci, da harshe. Wannan labarin maras tushe zai iya haifar da gagarumar tangarda ga dokar “bada tazara” wadda take a matsayin hanyar kariya ga COVID-19, musamman ma a kauyuka, lunguna da unguwanninmu na gargajiya.


A mafi yawancin lokuta, ana amfani da man kadanya ne a cikin man shafawa na fata, kuma yana dauke da sinadaran kitse (triacylglycerols) wadanda sukan bambanta bisa ga yanayin asali ko hanyar da aka hada shi man kadanyan. Su wadannan sinadaran kitsen sun kunshi sterik, falmitik, oliyek da kuma lainolek. Kuma bugu da qari, a kimiyyance, gabadaya wadannan sinadarai basu da wasu halayya ko dabi”ar da aka sani wanda zai bada kariya ga kwayar halitttar bacteriya, bairus da kuma sauransu. Don haka, wannan zai iya kasancewa sahihin zance na farko a kimiyyance da kan zama hujja kwakkwara cewa man kadanyan na kashe kwayar cutar coronavirus ba gaskiya ba ce. A zancen gaskiya dai babu wani bayani na kimiyya wanda ya nuna cewa man kadanya na iya kashe kowanne irin kwayar virus, ballantana ma COVID-19 wacce ta kasance sabuwa da ba’a santa sosai ba.

Covid 19

Amma sai dai da akwai wani binciken ilmi da aka nuna cewa, adadi kadan na man kadanya na kunshe cikin wani magani da yake kan gwaji akan Herpes Simplex Virus (HSV) amma har yanzu ba’a bayyana sakamakon binciken ba. A takaice, ko da sakamakon ya bayyana to zai yi matukar wahala a alakanta sakamakon HSV din da COVID-19. Saboda hanyoyin yaduwar HSV da COVID-19 da launinsu wajen samuwa sun bambamta. A saboda haka, duba da abinda yake faruwa na amfani da man kadanya a matsayin magani don kariya ga COVID-19, za’a ga cewa shirme ne (yin hakan) da kuma rashin sanin  ilmin kimiyya. Baya da haka, idan aka ajiye zancen rashin hujjar a kimiyyance a waje daya, wani abin takaicin da aka samu daga irin wadannan bayanai marasa tushe shine, wai harda hanci a cikin guraren da ake shafa shi man kadanyan. To shi wannan danyan aikin zai iya kara jawo yawaitar shigar sinadaran kitse cikin jiki wanda kan iya cutar da mutane masu alamun kamuwa da cututtukan zuciya.


A harsashe da bincike irin na ilimin kimiyya, ana iya zargin cewa wasu kananun sinaradai a cikin man kadanya kamar su finoliks, tiraitafins na iya kashe kwayar cutar kuma masu yada labaran nan maras tushe na iya fakewa da hakan, a matsayin hujja. Tabbas, akwai wani binciken wanda ya bayyana cewa irin wadannan kananun abubuwan cikin man kadanya kamar su katecin suna da dabi’ar maganin bairos, amma saidai kuma hujjojin da aka samu akan binciken basu da tasiri sosai da har za’a iya yin (irin wannan) magana ta shirme akan maganin (wannan) coronavirsu din. Hakika babu wani bincike na kwarai wanda yake alakanta wadannan sinadaran da sabuwar cutar COVID-19 da ake zance. Kamar yadda aka bayyana a baya, zai yi matukar wahala a dogara da sakamakon binciken da aka samu akan dabi’un wadannan sinadaran akan sauran virus zuwa ga COVID-19. Saboda haka, zargin cewa wadannan kananun abubuwan cikin man kadanya zasu iya maganin COVID-19, bai inganta ba a  kimiyyance.


A karshe, yin amfani da man kadanya a matsayin matakin kariya ga yaduwar COVID-19 karya ce, kuma bashi da tushe a kimiyyance. A yanzu dai (zamu iya cewa), bada tazara, wanke hannaye da hand sanitaiza. da kuma amfani da takunkumin hanci da baki, sune hanyoyi masu inganci wajen kariya daga yaduwar wannan cutar.


Mohammed Auwal Ibrahim (PhD) dai babban malami ne kuma mai bincike a sashin Biochemistry, na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, a Najeriya, sannan yanzu yana aiki as a matsayin mai bincike na JSPS a sashin tsara magani bisa taswira ta cibiyar kimiyya da fasahar masana”antu dake, Tsukuba, Japan.

bottom of page