top of page

SHAWARA GA JAMA'A MASU SHACI FADI AKAN CUTAR MURAR MASHAKO CORONAVIRUS (COVID-19)

Dr Adamu Abubakar Sadeeq and Zaid Muhammad

Wednesday, 1 April 2020

Shin Kwayar cutar Murar Mashako (COVID-19) zata iya yaɗuwa a wuraren dake da yanayi zafi?


Shaidu nanu ana iya yaɗa kwayar cutar Murar Mashako (COVID-19) a cikin dukkan yanayi na zafi ko Hamada. Bisa la’akkari da hakanne yasa, ɗaukan matakan kariya a idan kuke zaune, ko kuma idan kunyi balaguro zuwa yankin da aka tabbatar da annobar COVID-19 keda mahimmanci.  Hanya mafi kyau don kare kanka daga cutar murar mashako (COVID-19) shine ta tsaftace hannayenka akai-akai ta hanyar wankesu. Yin hakan, kan kawar da ƙwayoyin cutar da ke kan hannunka, domin ana kamuwa da cutar idan mutum ya taba ido,baki ko hanci da hunnun dake ɗauke da ƙwayar cutar.Tsananin sanyi da dusar ƙanƙara baya kashe ƙwayar cutar murar mashako (COVID-19)


Babu wani dalili da ya tabbatar da cewa yanayin sanyi na’iya kashe ƙwayar coronavirus ko wasu nau’in cututtukan ma. Yanayin zafin jikin ɗan adam, na yau da kullun yana kasancewa ne kusan 36.5 ° C -37 ° C, a ma’aunin  na selsiyos ba tare da la'akari da yanayin da ake ciki ba na zafi ko sanyi. Hanya mafi inganci don kare kanka daga sabon ƙwayar cutar coronavirus shine ta tsaftace hannayenku akai-akai tare da amfani da mai na tsaftace hannu “hand sanitizer” ko kuma wankesu da sabulu da ruwa.Wanka da ruwan ɗumi baya zama kariya akan ɗaukar cutar murar mashako


Wanka da ruwan ɗumi ba zai hana ka kamuwa da COVID-19 ba. Kasani cewa Yanayin zafin jikinka na yau da kullun ya kasance kusan 36.5 ° C zuwa 37 ° C, ba tare da la’akari da zafin ruwan da kayi wanka dashi ba. Hasali ma, wanka da ruwan zafi mai tsananin gaske yana iya cutarwa, saboda yana iya kancewa lahani ga jiki. Hanya mafi kyau don kare kanka daga COVID-19 shine ta tsaftace hannayenka akai-akai. Ta yin hakan, ka iya kawar da ƙwayoyin cuta da ke kan hannunka kuma ka guji kamuwa da cutar wanda zai iya faruwa ta hanya taɓa idanunka, bakinka ko hanci.Sabuwar cutar Coronavirus ba’a taba ɗaukar ta hanyar cizon sauro.


Zuwa yanzu dai babu wani bayani ko shaida da ke nuna cewa sauro na iya yada ƙwayar cutar Coronavirus. Sabuwar cutar coronavirus, cuta ce dake bin iska wacce take yaɗuwa ta hanyar fitar yawu lokacin da mai dauke da cutar yayi  tari ko hattishawa. Don kare kanka, tsaftace hannayenka akai-akai tare da shafa mai na tsaftace hannu ko kuma a wanke su da sabulu da ruwa. Sa’annan, a guji kusanci da duk wanda yake tari ko hattishawa.Yaya ingancin na’urar  gwajin dumin jiki don gano masu ɗauke da cutar murar  mashako (coronavirus)?


Na’urar gwajin dumin jiki na gano yanayin zafin jiki ne ga wanda suka kamu da sabuwar ƙwayar cutar murar mashako (COVID-19). Koyaya, na’urar gwajin baza ta iya gano mutanen da suka kamu da cutar ba, amma ba su kamu da zazzaɓi ba. Wannan na faruwa ne tsakanin kwanaki biyu zuwa goma kafin mutanen da suka kamu da cutar su kamu da zazzaɓi.Shin allurar rigakafin cutar sanyin na’iya bada kariya ga sabuwar cutar coronavirus?


A'a. Alurar rigakafin cututtukan huhu, ba su bada kariya daga sabuwar Kwayar cutar. Murar mashako  wacce akafi sani da corona virus sabuwa ce kuma tana buƙatar maganin ta na musam man. Masu binciken suna ƙoƙarin haɓaka rigakafi akan  cutar a inda hukumar lafiya ta duniya ke tallafawa ƙoƙarin su. Kodayake waɗannan alluran rigakafin ba su da tasiri a kan coronavirus, yin rigakafin cututtukan numfashi nada mahimmaci don kare lafiyar ku.Shin wanke hanci da ruwan gishiri zai iya hana kamuwa da cutar covid 19?


A'a. Babu wata hujja da ke nuni kan cewar yin hakan na kare mutane daga kamuwa da cutar Covid-19. Duk da cewar bincike ya nuna amfani da ruwan gishiri wajen shace hanci na iya taimaka wa mutane su  murmure da sauri daga mura na yau da kullun. Amma babu binceken dayayi nuni kan yin hakan na  hana kamuwa da cututtukan numfashi irin dangin coronavirus.


Covid 19

Shin hadiyar tafarnuwa na iya hana kamuwa da cutar na coronavirus?

Tafarnuwa abinci ne mai ƙara ƙoshin lafiya wanda ƙila yana da wasu abubuwan masu inganta garkuwar jiki. Amma, babu wata hujja bayan barkewar annobar murar mashako (Covid-19)  daya nuna cin tafarnuwa na iya kare mutane daga kamuwa da coronavirus.


Shin coronavirus kan kama tsofaffi ne kawai, ko kuma matasa ma suna iya saurin kamuwa?

Mutane na kowane irin rukunin shekaru na iya kamuwa da sabon coronavirus.Tsofaffi, da mutanen da ke dauke da wasu cututtuka (kamar asma, ciwon sukari, cututtukan zuciya) suna  kasancewa cikin haɗarin kamuwa da ƙwayar cutar. Hukumar lafiya ta duniya ta shawarci mutane na kowane rukuni su dauki matakai don kare kansu daga kamuwa daga cutar, alal misali ta bin kyakkyawan tsabtace hannun da kuma tsabtace abunda suke shaka.


Shin maganin rigakafi ƙwayoyin cututtuka nayau da kullum yana da tasiri wajen hanawa da kuma magance  cutar coronavirus?

A'a, maganin rigakafi ƙwayoyin cututtuka nayau da kullum baya aiki akan cutar coronavirus. Sabuwar coronavirus, cuta ce kuma sabili da haka, bai kamata a yi amfani da maganin rigakafi azaman hanyar rigakafi ko maganin taba.


Shin akwai takamai man magunguna don hana ko warkar da sabuwar coronavirus?

Har ya zuwa yau, babu takamaiman maganin da ake amafani dashi don dakile coronavirus. Duk da hakan, waɗanda ke fama da kwayar cutar ya kamata su sami kulawa daya dace don sauƙaƙe alamomin cutar, kuma waɗanda ke da ciwo mai tsanani ya kamata su sami ingantaccen kulawa. Ana kan bincike akan sababbin hanyoyin da salon jinya, kuma za a gwada sune ta hanyar gwaji na asibiti. Hukumar lafiyata duniya na taimakawa don hanzarta gudanar da binciken da kuma ci gaba wajen shawo kan cutar tare gudumuwar abokan hadin gwuiwar ta.


Adopted from https://www.who.int/emergencies/diseases/novel-coronavirus-2019/advice-for-public/myth-busters


Translated to Hausa by:

Adamu Abubakar Sadeeq, PhD, FASLN

Human Anatomy Department, Neuroscience Unit,

Ahmadu Bello University,Nigeria.

aasadeequ@gmail.com aasadeeq@abu.edu.ng   

+2348038250628


Zaid Muhammad, FASLN

Human Physiology Department,

Yobe State University, Damaturu, Nigeria.

Muhammadzayd42@gmail.com

+2348036636605


bottom of page