top of page

SHAN RUWAN DUMI HADE DA ROBB BA YA KASHE CORONAVIRUS (COVID-19)

Dr Adamu Abubakar Sadeed FASLN

Thursday, 2 April 2020

Akwai saƙon rashin fahimtar cutar murar mashako wato coronavirus da ake yaɗawa ta  kafofin sada zumunta: cewar shan ruwan dumi, gauraye da Robb, yana kashe Coronavirus (COVID-19). Kul, Wannan ba gaskiya bane.



Sakon da aka fi yaɗawa ta shafukan  sada zumunta shine:

"Don Allah, ina rokon ku, kada ku barwa kanku, zaku iya ceton rayuka game da Coronavirus ne. Waɗannan su ne alamomin Coronavirus: 1. Ciwon makogwaro 2. Bushewar makoshi da tari 3. Ciwon ciki 4. yawan guɗawa. Da fatan idan kun lura da ɗaya daga cikin waɗannan alamomin a cikin ku, ku yi sauri a sami ruwan zafi, ku haɗa da Robb ku sha. Domin ƙwayar cutar takan tsaya a cikin makogwaron mutum na aƙalla awanni goma sha biyu. Idan ba ku yi kamar yadda aka umurce kuba ba ko kuma bin shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) akan hakan, to a wannan  lokacin ne kwayar cutar za ta sami dama ta shiga cikin garkuwar jikinkku da sashin jikinku, saboda garkuwan jikin ku yayi rauni, zai sa ba za’a rayu sama da mako biyu ba a duniya. "



BISA GA BINCIKEN MU: WANNA LABARIN KANZON KUREGE NE


Shin shan ruwan dumi haɗe da Robb yana da amfani don kariya ga  COVID-19?


Ana amfani da maganin shafawa na Robb yawanci ne don taimakon rage sanyi na yau da kullun, cushe war hanci, ciwon kai da ciwon  jiki. Babu wata hujja da ta nuna cewa shan Robb tare da ruwan dumi yana kashe coronavirus. Madadin haka, wannan na iya haifar da mummunar matsalar rashin lafiya. Robb maganin shafawane ba’a haɗiyar shi ko sanya shi a cikin hanci,don haka a kula. Yawancin maganin shafawa na Robb sun ƙunshi sinadarai masu hadari, Idan aka yi amfani da  abinda ya wuce kima, duk wadannan sinadaran na iya illatar wa tare  da yin tasiri ga lafiyar mu. Lokacin da aka haɗiyi maganin shafawa na Robb, zai iya zama haɗari ga lafiyar ku, kuma wasu daga cikin abubuwanda ke ciki na iya haifar da mutuwa idan an yi amfani dashi fiye da kima.



Shin in mutum yaji alamomin cutar, wataƙila ya kamu da cutar ne. Ko Wannan gaskiya ne?


Dangane da binciken da aka buga a mujallar aikin likitoci, nacewa matsakaicin alamun COVID-19 yana farawa ne cikin kwanaki biyar. Binciken ya nuna cewa kusan kashi 97.5% na mutanen da suka kamu da cutar, na nuna  alamu ne a cikin kwanaki shaya daya zuwa sha biyu  da kamu warsu. Wannan yana nuna cewa lokacin da mutum ya fara nuna alamun cutar kuma aka tabbatar yana da cutar, hakan ya nuna cewa yana dauke da cutar na  tsawon kwanaki ne.

Covid 19

Shin cutar COVID-19 kan tsaya acikin makogwaro harna tsawon sa’a goma sha biyu?

Babu wata shaidar data nuna cewa kwayar cutar kan zauna a cikin makogwaro har tsawon awanni sha biyu. Kwayar cutar tana zaune a cikin ma’adanin rayuwar ɗan adam (cell), ba kawai tana zaunene cikin makogwaro ba, a inda shan ruwan dumi da robb zai kore ta. Farfesa Trudie Lang na Jami'ar Oxford ya ce "babu wani tsarin nazarin halittu" wanda ya goyi bayan ra'ayin cewa zaku iya wanke kwayar cutar numfashi ko coronavirus  daga cikin ku a matsayin ku kashe ta."


Shin hukumar lafiya ta duniya (WHO) ce taba da shawarar yin hakan.

A'a! Ga matakai bakwai na WHO don hana yaduwar COVID-19 (https://youtu.be/8c_UJwLq8PI)


Adopted; https://www.scicomnigeria.org/covid-19/Drinking-Warm-Water-and-Robb-Ointment-Does-Not-Kill-Coronavirus-(COVID-19)


Translated to Hausa by:

Adamu Abubakar Sadeeq, PhD, FASLN

Human Anatomy Department, Neuroscience Unit,

Ahmadu Bello University,Nigeria.

aasadeequ@gmail.com aasadeeq@abu.edu.ng

+2348038250628


bottom of page