top of page

Murar Mashako - COVID-19: Menene Manufar Hana Yin Taron Jama'a Domin Wannan Sabor Cuta

Dr Harun Rashid

Tuesday, 31 March 2020

Kamar yadda muka sani cewa cutar murar mashako (wato COVID-19 a turance), cuta ce dake kama hu-hun dan Aadam kuma ta masa lahani har ta iya kai ga halaka. Wanna cuta ta samo asali ne daga garin Wuhan a kasar Sin, amma a halin yanzu ta zama annoba da ta mamaye akasarin kasashen duniya [1]. Tambayar da za mu amsa muku ayau ita ce; menene manufar hana yin taro, duk da babu cutar a jihar ka ko jihar ki?


Wannan tambaya ce wandda duk mutum mai nazari zai yi, kuma ta chanchanci a war-ware domin mu fahimta, mu gamsu, kuma mubi umarnin hukumomi kamar yadda aka kafa. Hakika wannan cuta ba’a tabbatar da ita ba a jihohi da dama amma kuma an dauki tsauraren matakan hana yin taro da yin tafiya da-dai sauran su [2]. Menene manufofin daukan wannan matakai atakaice [3]? Ga nan wasu daga cikin wannan manufofin kamar haka: -


1. Cutar bata da fuska; akasarin mutanen dake dauke da kwayar cutar murar mashako basa nuna wani irin nauyin rashin lafiya ko alamu har sai bayan kwana 5 zuwa 11 da kamuwa da wannan cutar. Abin nufi anan shi ne, za mu iya daukar cutar daga wajen masu ita ba tare da mun sani ba, kuma hakazalika muma mu cigaba da yadawa al-umma ba tare da mun sani ba. Wannan kuma zai haifar da hatsari mai muni matuka cikin al-umma


2. Riga-kafi; a halin yanzu dai cutar mashako bata da magani ko allurar riga-kafi domin magance ta ko kariya daga kamuwa. Babban riga-kafi a wannan hali shine kiyaye kawunan mu ta hanyar bin dokokin da hukumar lafiya suka shar’anta. Shiga taro yanada hatsari matuka a wannan lokaci domin hakan na zama sanadi na yadawa mutane wannan cuta a bai daya. Ma’ana mutum daya kachal zai iya yadawa mutane 10 ko ma fiye da haka a bai daya.

Covid 19

Duk wanda ya kamu shima zai iya komawa gida ya yadawa iyalen sa kuma babu wanda zai san hakan har sai bayan alamomi sun fara bayyana bayan wasu kwanaiki. Hana shiga taro na sahun gaba a cikin jerin riga-kafin da hukumar lafiya ta shar’an ta a yau. Wannan ya hada da daurin-aure, suna, walima, makaranta, kasuwa, massalatai da coci. Idan wannan annoba ta wuce da iznin Allah, za mu cigaba da rayuwar mu kamar yadda muka saba idan muna cikin masu rai.


3. Wata kila makwocinka na da ita; hukumar lafiya har yanzu bata gama gwada mutanen da take tsammani na dauke da cutar nan ba. Wasu daga cikin su sunyi tafiye-tafiye a cikin Naijeriya kamar zuwa daurin aure da ziyarar ‘yan uwa da dai sauran su. A bisa wannan, kada mu shagalta da cewa babu wanda aka tabbatar yana dauke da wannan kwayar cutar a jihar mu ko garin mu. Ya kamata mu dauki izna daga kasashen duniya mu kuma bi umarnin hukuma.


Domin samun karin cikakken bayani akan wannan annoba ta murar mashako, ku karanata wannan rubuta da masana sukayi Murar Mashako (COVID-19) - . Ku cigaba da bin mu a shafin mu na yanar gizo.

Nassoshi;

  1. https://www.who.int/publications-detail/report-of-the-who-china-joint-mission-on-coronavirus-disease-2019-(covid-19)
  2. https://www.dailytrust.com.ng/as-cases-jump-to-70-large-gatherings-persist-in-states.html
  3. https://www.who.int/publications-detail/public-health-for-mass-gatherings-key-considerations


bottom of page